Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan mutanen da suka kamu da COVID-19 ya kai 566 a Ghana
2020-04-13 09:27:44        cri
Hukumar lafiyar kasar Ghana GHS ta sanar a ranar Lahadi cewa, an samu karin mutane 158 da suka kamu da cutar COVID-19, hakan shi ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar a kasar zuwa 566.

Hukumomin kasar sun danganta karuwar adadin da aka samu na wadanda suka kamu da cutar da irin matakan da aka dauka wajen gano mutanen da suka yi mu'amala da masu dauke da cutar a fadin kasar.

Baki daya, hukumomin lafiyar kasar Ghana sun yiwa mutane 37,954 gwaji, yayin da aka samu mutane 566 dauke da cutar.

Daga cikin adadin, mutane 8 sun mutu, yayin da mutane 4 an tabbatar sun warke daga cutar.

Shugaban kasar Ghana Nana Addo DankwaAkufo-Addo ya sanar tun da farko a ranar Lahadi cewa an tsawaita dokar hana taruwar jama'a a duk fadin kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China