Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsoffin 'yan siyasan kasa da kasa sun yi kira ga kasashe daban daban su hada gwiwa don tinkarar COVID-19
2020-04-11 20:08:42        cri
Wani labarin da cibiyar nazarin tsare-tsaren raya kasa da kirkiro sabbin fasahohi karkashin cibiyar nazarin kimiyya ta Sin ta gabatar, ya ce wani abokin huldarta, kuma tsohon firaministan Birtaniya, James Gordon Brown, ya samu yin hadin gwiwa da wasu shahararrun tsoffin 'yan siyasa da masana 165, inda suka rubuta wata wasika ga kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta G20. Cikin wasikar sun yi kira ga mambobin kungiyar G20, su fara daukar matakan hadin gwiwa a cikin kwanaki masu zuwa, ta yadda za a samu damar tinkarar barazanar da cutar COVID-19 ta haifar ga lafiyar jama'ar kasashe daban daban, gami da tattalin arzikin duniya.

Ban da haka, sun bayyana goyon baya ga hukumar lafiya ta duniya WHO, da ta ci gaba da jagorantar ayyukan dakile yaduwar cutar a duniya. Haka kuma an bukaci a dauki wasu matakai cikin sauri don neman farfado da tattalin arzikin duniya. Hakan, a cewar tsoffin 'yan siyasa da masana na kasashe daban daban na bukatar samun alkawarin da shugabannin kasashen daban daban za su yi don tabbatar da samar da isashen kudin da ake bukata, wanda yawansa ya zarce karfin dukkan kungiyoyin kasa da kasa. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China