Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Lura da bullar COVID-19 a karon farko na da muhimmanci ga yaki da cutar a Afirka
2020-03-09 20:11:58        cri
Jami'ar tsare tsare game da ayyukan gaggawa na lafiya, ta ofishin shiyya na hukumar WHO Mary Stephen, ta ce abu ne mai muhimmanci ga kasashen Afirka, su lura da bullar cutar numfashi ta COVID-19 a karon farko na shigar ta kasashen su.

Mary Stephen, ta yi wannan tsokaci ne yayin wata tattaunawar baya bayan da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, inda ta ce dukkanin kasar da ta bari cutar ta yadu, ba tare da sanin mutum na farko da ya shigar da ita ba, zai zame mata abu mai wuya ta iya shawo kan ta cikin hanzari.

Stephen ta kara da cewa, kasashen Afirka 27 na da ikon ganowa, da kuma tabbatar da bullar cutar, sun kuma tanaji cibiyoyin ko ta kwana, da na tsara ayyuka, kana sun kafa matakan shiri, da na hanzarta ayyuka a matakin kasa baki daya.

Jami'ar ta ce bullar cutar a Afirka ta biyo bayan shigar baki ne daga wajen nahiyar, hakan na kuma da nasaba ne da yawan zirga zirgar al'umma tsakanin kasashen da cutar ta yadu, da kuma wasu yankunan Afirka.

Daga nan sai ta jinjinawa matakan da kasar Sin ta dauka, wadanda suka haifar da manyan nasarori, duba da cewa kawo yanzu, ba a samu wani dan kasar Sin da ya shiga nahiyar dauke da kwayar cutar ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China