2020-02-29 17:01:04 cri |
Da yake jawabi a jiya, Darakta Janar na hukumar, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce kwararru masu nazarin yanayin cututtuka na hukumar, sun yi ta bibiyar yanayin cutar akai-akai, kuma a yanzu, sun daga matakain hadarin yaduwa da tasirin cutar COVID-19 zuwa mai hadari sosai a duniya.
A ranar Alhamis ne Kasashen Denmark da Estonia da Netherlands da Nijeriya suka tabbatar da samun bullar cutar a karon farko, kuma dukkansu na da alaka da kasar Italiya. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China