2020-02-28 12:17:13 cri |
A Jumma'a ne hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO ta shirya taron manema labaru dangane da annobar cutar numfashi ta COVID-19, inda Michael Ryan, jami'in hukumar mai kula da ayyukan kiwon lafiya na gaggawa ya ce, yanzu an takaita shirya manyan taruka da bukukuwa, sakamakon barazanar yaduwar annobar da ake fuskanta. Amma ana gudanar da ayyyukan share fage na gasar wasannin Olympics ta Tokyo kamar yadda aka tsara. Ba za a tsai da kuduri nan ba da dadewa ba, kan ko za a sauya gasar ko a'a ba.
Jami'in ya kara da cewa, hukumar tana hada kai da kwamitin kula da ayyukan wasan Olympics na kasa da kasa da kuma kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta Tokyo, wajen kimanta barazanar da za a fuskanta da kuma ba da shawara. A baya an samu barkewar annoba a lokacin gasar wasannin Olympics, kana an gudanar da wasu wasannin yayin da ake sa ido a kansu. Hukumar ta WHO za ta ci gaba da bai wa kwamitocin 2 shawara game da matakin da ya dace a dauka.
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China