2020-03-08 16:15:26 cri |
Tedros ya bayyana hakan ne a lokacin ganawa da Chen Xu, wakilin din din din na kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva (UNOG).
Ya bayyana farin cikinsa da kuma nuna yabo ga gwamnatin kasar Sin, wacce take kokarin magance wahalhalun da take fuskanta, bisa jin kan da ta nuna wajen tallafawa kasashe masu tasowa a wannan matsanancin yanayin da ake ciki na yaki da annobar a duk duniya.
Mista Tedros ya ce, hukumar WHO za ta ci gaba da yin aiki tare da kasar Sin domin ingiza ayyukan hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa wajen magancewa da kandagarkin cutar.
A lokacin ganawar, Chen ya ce, ayyukan magancewa da kandagarkin cutar COVID-19 a kasar Sin yana samun gagarumar nasara da kuma kyakkyawan sakamako bisa ingantattun matakan da gwamnatin Sin da al'ummar kasar suke dauka.
Kwayar cutar tana shafar daukacin kasashen duniya, in ji wakilin na kasar Sin, ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da hukumar WHO da kuma dukkan bangarori waje yakar annobar cutar.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China