Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta sakawa jami'an lafiyar da suka yi yaki da cutar coronavirus
2020-02-14 19:58:19        cri
Hukumomin kasar Sin, sun fitar da wasu tsare tsare na musamman, domin sakawa jami'an lafiyar da suka ba da gudummawa, a yakin da kasar ke yi da cutar numfashi ta coronavirus.

A cewar mataimakin darakta a hukumar lafiyar kasar Sin Zeng Yixin, an tanaji sakayya da ta dace, ga jami'an lafiyar da suka harbu da cutar, da tanajin musamman ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan muhimmin aiki, karkashin inshorar kare hadurra ta ma'aikata.

Zeng Yixin ya bayyana hakan ne a Jumma'ar nan, yayin wani taron manema labarai. Ya ce baya ga wancan tanadi, an kuma tsara samar da kudaden alawus, da rahusa kan wasu kayayyaki, ga likitoci da nas nas, wadanda suka yi aiki gadan gadan yayin wannan annoba.

A nasa tsokaci yayin taron manema labaran, mataimakin ministan kula da harkokin kwadago da tsaron al'umma na kasar Sin Zhang Yiquan, ya ce jami'an lafiya, da rukunonin ma'aikata daban daban, da suka ba da muhimmiyar gudummawa wajen bincike, da samar da rigakafi, da ma sauran wasu fannoni masu nasaba da hakan, za su samu lambobin yabo da na karramawa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China