Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta tura sama da ma'aikatan lafiya dubu 11 zuwa Wuhan
2020-02-07 20:17:18        cri
Hukumomin lafiya a kasar Sin sun bayyana cewa, an tura sama da ma'aikatan lafiya dubu 11, ciki har da kwararrun ma'aikatan kasar a fannin kulawar gaggawa, zuwa birnin Wuhan, inda wannan annoba ta bulla.

Guo Yanhong, jami'a a hukumar lafiya ta kasar, ita ce ta bayyana haka yayin taron manema labarai a nan birnin Beijing. Ta ce, daga cikin wadannan jami'an lafiya da aka tura, sama da dubu 3 daga cikinsu, likitico ne da nas-nas da suka kware a fannin kulawar gaggawa. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China