![]() |
|
2020-02-07 20:12:16 cri |
Rahotanni daga Wuhan na kasar Sin, birnin da annobar cutar numfashi da ta bulla na cewa, ana tantance dukkan mazauna birnin don tabbatar da cewa, duk wanda aka tabbatar ko maras lafiya da ake zaton ya kamu da cutar an gano shi an kuma ba shi kulawar da ta dace.
Wani babban jami'i a yankin, shi ne ya tabbatar da hakan, yayin taron manema labarai game da matakan yaki da cutar. Ya kuma lashi takwabin cewa, duk wanda ya ki ba da hadin kai zai yabawa aya zaki.
An kuma ba da umarnin cewa, za a dauki matakan da suka dace, don zakulo marasa lafiya da aka tabbatar sun kamu da cutar ko kuma ake zaton sun kamu da kwayar cutar, da sanya ido kan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar da ma marasa lafiya dake fama da zazzabi. (Ibrahim Yaya)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China