Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na daukar matakai don tabbatar da isassun kayayyaki da zaman odar al'umma
2020-02-06 13:53:43        cri

Sin na daukar matakai iri daban-daban, don tinkarar yaduwar cutar numfashi, ta yadda za a ba da tabbaci ga samar da isassun kayayyaki, da goyon bayan ayyukan kamfanoni, da biyan bukatar jama'a.

An ce, saboda sufurin kayayyakin da ake matukar bukata, ma'aikatar zirga-zirga ta kasar Sin, ta kafa hanyoyin musamman na kaucewa cikas.

Ya zuwa yanzu, kamfanoni mallakar gwamnati suna yin iyakacin kokarin samar da abun rufe baki da hanci, da rigar kandagarki, da magungunan kashe kwayoyin cuta, da dai sauran na'urorin likitanci. Haka kuma, bankin raya sha'anin noma, ya kebi wata hanya ta musamman don samarwa kamfanoni fiye da 60 rancen kudi cikin gaggawa, wadanda yawansu ya kai fiye da RMB Yuan biliyan 5, don goyon bayan aikin samar da kayayyakin tinkarar wannan mumunar cutar.

Game da wasu kananan kamfanoni wadanda cutar ke haifar musu da babbar illa kuwa, gwamnatocin wurare, na samar da manufofin gatanci don ba su tallafi a wannan lokaci. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China