Kasar Sin za ta inganta aikin yaki da annobar cutar numfashi ta fuskar hada-hadar kudi
Wani jami'in hada-hadar kudi na kasar Sin ya bayyana yau Jumma'a a nan Beijing cewa, kasar Sin ta ware kasafin kudin Sin RMB yuan biliyan 66.74 wajen yakar annobar cutar numfashi, a kokarin samar da isassun kudaden shawo kan annobar a sassa daban daban a kasar. Haka kuma, hukumomi masu ruwa da tsaki na kasar sun fito da matakai da dama domin ba da tallafin kudi wajen yaki da annobar, a kokarin ba da tabbaci a fannonin zaman rayuwar jama'a da ci gaban tattalin arzikin kasar. (Tasallah Yuan)
Labarai masu Nasaba