Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Gwamnatocin kasashe 21 da UNICEF sun ba da tallafin kayayyakin yaki da yaduwar cutar numfashi
2020-02-06 11:06:52        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying, ta bayyana a jiya Laraba cewa, ya zuwa tsakar wannan rana, gwamnatocin kasashe 21, da asusun tallafawa kananan yara na MDD wato UNICEF, sun baiwa kasar Sin tallafin kayayyakin yaki da yaduwar cutar numfashi, kuma kasarta za ta ci gaba da samar da bayanai ga sauran kasashe bisa ka'idar gudanar da ayyuka a bayyane, da adalci don inganta hadin kansu.

A gun taron manema labarai da aka yi a wannan rana kuma, Hua ta ce, Sin na dogaro da karfin kanta wajen tinkarar wannan cuta, a sa'i daya kuma, tana maraba, da kuma godiya ga sahihiyar fahimta, da goyon baya da taimako da kasashen duniya ke ba ta.

Hua ta kara da cewa, ya zuwa tsakar wannan rana, gwamnatocin kasashe 21 da kuma UNICEF, sun baiwa kasar Sin tallafin kayayyakin yaki da cutar. Kasashen dai sun hada da Koriya ta kudu, Japan, Thailand, da Malaysia, da Indonesiya, da Kazakhstan, da Pakistan da Jamus. Sauran sun hada da Birtaniya, da Faransa, da Italiya, da Hungary, da Belarus. Sai kuma kasashen Turkiya, da Iran, da daular Larabawa, da Aljeriya, da Masar, da Austriliya, da New Zealand da dai sauransu.

A sa'i daya kuma, karin kasashe da dama sun bayyana burinsu, na baiwa kasar Sin taimako. Ban da wannan kuma, aminai na kasashe daban-daban, suna ta mika sakonsu na goyon baya ga gwamnatin kasar Sin, game da yakin da take yi da cutar ta hanyoyin daban-daban. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China