Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu karuwar mutane 3,235 da suka kamu da cutar coronavirus
2020-02-04 10:25:58        cri
Hukumomin lafiya na kasar Sin sun ce yawan sabbin wadanda suka kamu da cutar numfashi ta coronavirus a ranar Litinin ya kai mutane 3,235, kana karin mutane 64 sun rasu sakamakon hakan. Sabbin wadanda suka harbu da cutar dai sun kunshi jama'ar yankunan lardun kasar 31, da kuma rukunin ma'aikatan kwadago na jihar Xinjiang. To sai dai kuma a wannan karo, dukkanin wadanda suka rasu 'yan lardin Hubei ne, lardin da a nan ne cutar ta fara bulla.

A daya bangaren kuma, yawan wadanda cutar ta yi tsanani a jikin su a jiya Litinin sun kai mutane 492, yayin da wasu mutanen 157 suka warke aka kuma sallame su daga asibiti.

Bisa kididdiga, jimillar wadanda suka kamu da wannan cuta ya zuwa ranar Litinin sun kai mutane 20,438, ciki hadda jimillar mutane 425 da suka rasu.

Kaza lika kawo yanzu an sallami jimillar mutane 632 daga asibiti bayan sun warke daga wannan cuta. Hukumar lafiyar kasar Sin ta ce an sanya ido kan mutane da suka yi cudanya da wadanda cutar ta shafa, da yawan su ya kai 221,015, ciki hadda mutane 12,755 da aka kammala tantance su, yayin da 171,329 ke ci gaba da samun kulawar jami'an lafiya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China