Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gano sabbin wadanda suka kamu da cutar coronavirus 3,694 da karin mutum 73 da cutar ta hallaka
2020-02-06 10:43:36        cri
Hukumomin lafiya na kasar Sin sun ce a jiya Laraba, an samu karuwar mutane 3,694 da suka kamu da cutar numfashi ta coronavirus, yayin da kuma wasu karin mutane 73 suka rasu bayan fama da cutar.

Adadin dai ya kunshi na wadanda cutar ta harba daga yankunan lardunan kasar Sin 31, da kuma rukunin ma'aikata sojoji masu ba da taimako a jihar Xinjiang. Baya ga wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, akwai kuma wasu karin mutanen 5,328, da ake kokarin tantance matsayin su.

Hukumomin lafiyar sun ce a ranar Larabar, mutane 640 sun shiga matsanancin yanayin rashin lafiya sakamakon kamuwa da wannan cutar, a hannu guda kuma an sallami wasu mutane 261 daga asibiti bayan sun warke daga cutar.

Bisa jimilla, ya zuwa daren Laraba, adadin wadanda suka kamu da cutar a babban yankin kasar Sin ya kai mutum 28,018, yayin da jimillar wadanda suka rasu ya kai mutum 563.

Hukumar lafiyar kasar ta kuma ce, adadin marasa lafiya dake cikin matsanancin hali ya kai mutum 3,859, yayin da ake sanya ido kan wasu mutane da yawan su ya kai 24,702. Kaza lika jimillar mutanen da aka sallama bayan sun warke daga cutar sun kai mutum 1,153.

A daya hannun kuma, a daren ranar ta Laraba, an tabbatar da rahoton kamuwar mutane 21 da wannan cuta a yankin musamman na Hong Kong, kana ta hallaka mutum guda, yayin da cutar ta kama mutane 10 a Macao da mutu 11 a Taiwan. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China