![]() |
|
2020-02-05 11:19:20 cri |
Cikin wata sanarwa da mataimakiyar firaministan kasar Sun Chunlan, dake jagorantar tawagar ta fitar, ta bayyana muhimmancin aiwatar da tsarin da gwamnatin tsakiyar kasar Sin ya fitar, na shawo kan yaduwar wannan annoba cikin sauri. Ta ce ya zama wajibi a kara azamar aiki a lardin Hubei, musamman ma birnin Wuhan, inda cutar ta fi kamari.
Jami'ar ta kuma yi kira ga mahukuntan lardin, da su zage damtse wajen aiwatar da matakai daki daki, na kandagarki, da dakile yaduwar annobar, ta hanyar killace masu dauke da ita, da sanya ido kan wadanda ake da tantama a kan su, da masu fama da zazzabi, da makusantan masu dake da ita. A cewar ta, dole ne a shigar da daukanin sassa, da bangarorin al'umma cikin wannan muhimmin aiki.
Karkashin kulawar wannan tawaga ta musamman, tuni aka fara sauya wasu wuraren taruwar jama'a dake birnin Wuhan, zuwa cibiyoyin lura da masu dauke da wannan cuta. Cikin irin wadannan wurare, an mayar da wasu 3 zuwa asibitocin tafi da gidan ka, da suka samar da gadaje 3,800 domin kwantar da wadanda suka nuna alamu marasa tsanani, na kamuwa da cutar. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China