![]() |
|
2020-02-05 10:47:23 cri |
Hukumar lafiya ta kasar Sin, ta ce ya zuwa jiya Talata, an sallami jimilar marasa lafiya 892 da suka kamu da sabuwar kwayar cutar Corona daga asibiti, bayan sun warke.
Rohoton da hukumar lafiya ta kasar kan fitar a kullum, ya ruwaito cewa, an sallami mutane 262 daga asibiti a jiya Talata, bayan sun warke daga cutar numfashi ta corona, kuma 125 daga cikinsu na lardin Hubei. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China