Kasar Sin ta dauki matakan ba da jinya da rage mace-macen wadanda suka kamu da cutar numfashin da ta bulla a kasar
A yau Talata, mahukuntan kasar Sin sun kara daukar matakan inganta kwantar da marasa lafiya da rage mace-mace da ma wadanda ke kamuwa da annobar da ta bulla lardin Hubei dake tsakiyar kasar da ma Wuhan, babban birnin lardin. Wata sanarwa da aka bayar bayan kammala taron babban kwamitin kandagarki da ma hada yaduwar cutar na kwamitin tsakiya na JKS wanda Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya jagoranta, ta bayyana cewa, za a kara daukar matakai, don tabbatar da ganin an samar da kayayyakin kiwon lafiya na yau da kullum da ake bukata. (Ibrahim Yaya)
Labarai masu Nasaba