![]() |
|
2020-02-05 10:43:21 cri |
Hukumar lafiya ta kasar Sin, ta ce a jiya Talata, ta samu rahotannin dake cewa, akwai sabbin wadanda suka kamu da cutar Corona guda 3,887, daga larduna 31 da kuma rukunin ma'aikata sojoji masu ba da taimako a jihar Xinjiang. Haka kuma, akwai wasu 65 da suka mutu, dukkaninsu a lardin Hubei.
Har ila yau, hukumar ta ce a jiyan, akwai wasu mutane 3,971 da ake zargin sun kamu da cutar.
Ta ce jimilar wadanda suka kamu da cutar a babban yankin kasar Sin ya kai 24,324 ya zuwa jiya Talata, sannan jimilar wadanda suka mutu sanadiyyar cutar ya kai 490. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China