Kasar Sin ta bayar da izinin gaggauta shigo da kayayyakin yaki da yaduwar annobar cutar numfashi
Babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, ta kaddamar da alkaluma a shafinta na Intanet cewa, daga ranar 24 ga watan Janairu zuwa ranar 2 ga watan Febrairun bana, yawan kayayyakin yaki da yaduwar annobar cutar numfashi da kasar Sin ta saya daga ketare ya kai miliyan 240 baki daya, wadanda darajarsu ta kai kudin Sin RMB yuan miliyan 810, a cikinsu kuma akwai kayayyakin ba da kariya da yawan su ya kai kaso 75 cikin dari, wadanda darajarsu ta kai yuan miliyan 610, sun kuma hada da abubuwan rufe baki miliyan 220, da tufafin ba da kariya miliyan 2 da dubu 529, da tabarau din ba da kariya dubu 279.
An labarta cewa, hukumomin kwastam na kasar Sin sun kebe wuraren musamman domin baiwa kayayyakin yaki da yaduwar annobar izinin shiga kasa cikin gaggawa bisa ka'idojin musamman. (Tasallah Yuan)