Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi zai ziyarci kasashen Afirka biyar
2020-01-02 19:36:29        cri

Dan majalissar gudanarwar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, zai kai ziyara kasashen Masar da Djibouti, da Eritrea, da Burundi da Zimbabwe, tsakanin ranekun 7 zuwa 13 ga watan nan na Janairu.

Kakakin ma'aikatar wajen Sin Geng Shuang ne ya sanar da hakan a Alhamis din nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa. A cewar Geng, ziyarar ta wannan karo za ta kasance karo na 30 a jere, da ministan wajen Sin ke gudanar da ziyara a Afirka, a farkon ko wace shekara. Ya ce wannan kyakkawar al'ada ta Sin, na nuni ga irin muhimmancin da kasar ke dorawa, ga burin inganta dangantaka da nahiyar Afirka, wanda hakan ke shaida dankon kawance na tsawon lokaci tsakanin Sin da nahiyar Afirka.

Jami'in ya ce a bana ake cika shekaru 20 da kafuwar dandalin FOCAC, na tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, kana muhimmiyar shekara ce da a cikin ta, ake ci gaba da aiwatar da sakamakon kudurorin da aka cimma, yayin taron FOCAC na shekarar 2018 da ya gudana a birnin Beijing.

Geng ya kara da cewa, yayin wannan muhimmiyar ziyara, Wang Yi zai karfafa tattaunawa, da daidaita manufofi da sassan Afirka, domin bunkasa shawarar nan ta ziri daya da hanya daya, da daga matsayin abotar gargajiya dake tsakanin Sin da Afirka, tare da daga matsayin hadin gwiwar sassa biyu zuwa wani sabon mataki.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China