![]() |
|
2019-12-20 12:46:10 cri |
Bisa goron gayyatar da majalisar dokokin kasar Tanzania ta aike masa, Ji Bingxuan, mataimakin shugaban zaunannen kwamitin wakilan jama'ar kasar Sin NPC, ya kai ziyarar aikin kwanaki uku zuwa kasar Tanzania tun daga ranar Talata zuwa Alhamis.
Mista Ji, ya kuma halarci bikin kaddamar da wani aikin raya ci gaban al'ummma na kan hanyar siliki a Tanzania.
Bangaren kasar Tanzania ya yabawa kasar Sin sakamakon goyon bayan da take baiwa kasar na tsawon lokaci musamman wajen bunkasa tattalin arziki, da ci gaban zamantakewar al'ummar kasar Tanzania, kana ta bayyana aniyar ci gaba da karfafa hadin gwiwa da kasar Sin karkashin shawarar ziri daya da hanya daya BRI, da nufin zurfafa kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China