![]() |
|
2019-11-14 10:14:39 cri |
Manyan sassan da suka samu tagomashi a shekarar ta 2019, sun hada da na gine-gine, da noma, da hakar ma'adanai da fasa duwatsu, wadanda suka samar da ci gaban da ya kai kusan kaso 67.7 bisa dari.
A cikin kundin bayanai da bankin ya fitar, bayan karewar watanni ukun kusa da karshen shekarar nan, a cikin watan Satumba, bankin na BoT ya ce, hauhawar farashin kayayyaki bai zarce matsakaicin matsayin da kasar ta tsara, wato kaso 5.0 bisa dari ba.
Kaza lika darajar musayar kudin kasar ta daidaita a cikin watannin uku, inda matsakaicin farashin sa ke kan shillings 2,300.60 kan ko wace dalar Amurka daya, kasa da shillings 2,283.79 kan dala daya, a makamancin lokaci na shekarar 2018.
A daya bangaren kuma, ya zuwa karshen watan Satumbar bana, kasar ta gudanar da manyan ayyukan samar da ci gaba, daga basussukan waje da yawansu ya kai dala biliyan 22.17, sama da dala biliyan 21.92 da aka kashe a makamancin lokaci na shekarar 2018. (Saminu Hassan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China