![]() |
|
2019-07-22 10:00:30 cri |
Wata sanarwa da Daraktan yada labarai na fadar shugaban kasar, Gerson Msigwa ya fitar, ta ce Shugaba Magufuli ya nada George Simbabchawene a matsayin wanda zai maye gurbin January Makamba.
Sanarwa bata bayyana dalilan korar matashin ministan muhallin ba, wanda ya fara haramta amfani da jakar leda a kasar, dokar da ta fara aiki a hukumance a ranar 1 ga watan Yunin bana.
Haramta amfani da jakar leda na da nufin rage bolar robabi da rahotanni suka ce na gurbata teku da kasa, a wani mataki mai tada hankali. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China