![]() |
|
2019-09-28 16:58:00 cri |
Wang Yi, ya bayyana yayin taron muhawara karo na 74 na babban zauren MDD cewa, kasar Sin ba za ta taba yunkurin fadada kanta ba, kuma za ta ci gaba da bin ka'idar zaman daidaito a tsakanin kasa da kasa da kauracewa tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashe, kamar yadda dokar MDD ta tanada.
Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da daukaka manufar hulda da kasashen waje cikin lumana, bisa girmama cikakken 'yancin kai.
Bugu da kari, ya ce kasar ba za ta taba kaskantar da kanta ga wata kasa ba, haka zalika ba zata matsawa wasu kasashe lamba ba. Yana mai cewa kasar jajirtacciya ce wajen tsare muradu da halaltattun hakkokinta.
Ya ce samun ci gaba cikin lumana, wanda aka dade da sanyawa cikin kundin tsarin mulkin kasar, shi ne tubalin manufar huldarta da kasahen waje. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China