Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
HK ba wuri ne na fariya ga 'yan siyasar Amurka ba
2019-11-22 15:40:57        cri
Ba al'ummar Sinawa ne kadai suka nuna adawa tare da yin tir da labarin dake cewa majalisar dattawan Amurka ta yi muhawara tare da zartar da dokar kare hakkin bil Adama da tabbatar da demokuradiyya a HK ba, har ma da sauran al'ummomin kasa da kasa.

Wasu masu hangen nesa sun yi tsokaci game da yunkurin na 'yan siyasar Amurka, wanda ke kokarin amfani da batun na HK wajen danne kasar Sin, a sa'i daya kuma, yunkuri ne neman yin suna.

Sai dai, irin wannan mummunan aiki ba shi da wani fa'ida a wajen al'ummar Sinawa, in ban da ma su zubar da kimarsu a idon Sinawan.

Tom Fowdy, malami a Jami'ar Oxford ya ce dokar kare hakkin dan Adam da tabbatar da demokuradiyya ta HK yunkurin na amfana daga hadarin da mutane ke ciki, wanda ba shi da alaka da hakkokin bil Adama ko demokuradiyya.

Wannan mummunar manufa ce ta 'yan siyasar Amurka kan batun HK. Za mu so mu tunatar cewa, da ma can HK wani bangare ne na kasar Sin, ba wuri ne na fariya ga 'yan siyasar Amurka ba. Idan aka shiga wurin da bai kamata ba, to lamarin zai iya zama na ban dariya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China