Jakadan Sin ya yi Allah wadai da tsarin babakeren da Amurka ke dauka kan sararin samaniya
Kwamitin kwance damarar soja da tabbatar tsaron kasa da kasa na babban zauren MDD ya kira muhawara kan batun sararin samaniya a New York, helkwatar majalisar kwanan baya. Inda wakilin Sin a fannin kwance damarar soja Li Song, ya yi kira ga Amurka da ta yi watsi da tsarin babakere da ta dauka kan saranin samaniya, a maimakon haka, ta hada kai da kasashen duniya don mayar da hankali kan gujewar yin takara dangane da makamai a sararin samaniya, da nufin maido da zaman lafiya da kwanciyar hankalin wurin. Li Song ya kara da cewa, Sin na fatan kara hadin kai da bangarorin daban-daban don tabbatar da tunanin kafa kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya a sararin samaniya da taka rawarta wajen kiyaye zaman lafiya mai karko da tsaron bai daya a sararin samaniya. (Amina Xu)
Labarai masu Nasaba