Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan siyasan Amurka sun tsoma baki a harkokin wurare da dama
2019-11-21 14:50:03        cri

Dangane da yadda majalisar dattawan kasar Amurka ta zartas da shirin doka kan hakkin dan Adam da dimokuradiyya a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin a shekarar 2019, gidan rediyon "Muryar Yankin Mashigin Teku" karkashin babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya gabatar da sharhi a ranar 20 ga watan da muke ciki, mai taken "'Yan siyasan kasar Amurka sun tsoma baki a harkokin wurare da dama a duniya".

Sharhin ya ce, abin da majalisar dattawan Amurka ta yi ya mayar da baki fari, da sanya mutane cikin rudani bisa karyar da ta yi, kana tsoma baki ne a harkokin cikin gida na kasar Sin. Don kaka,ya saba wa dokokin kasa da kasa da manyan ka'idojin raya hulda a tsakanin kasa da kasa. Al'ummomin duniya sun kara fahimtar ainihin halayen wadannan 'yan siyasan Amurka marasa kunya da kuma mummunar makarkashiyarsu ta neman dakatar da ci gaban kasar Sin.

Sharhin ya kara da cewa, duk wuraren da wadannan 'yan siyasan Amurka suka tsoma baki a ciki, ba a samun kwanciyar hankali. Babu wanda bai san irin abubuwan da suke faruwa a kasashen Iraki, da Ukraine, da Syria ba. Yanzu kuma sun tsoma baki a harkokin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin. Inda suka kitsa tayar da tarzoma a yanki na Hong Kong, ta yadda hakan ka iya dakatar da ci gaban kasar Sin.

Sharhin ya jaddada cewa, 'yan siyasan Amurka sun kudiri aniyar ganin batun Hong Kong ya zama mai sarkakkiya. Amma a zahiri, ba za su iya hana ci gaban kasar Sin ba, a karshe dai za su illata moriyar kasarsu ta Amurka. Idan Amurka ta ci gaba da yin hakan, tabbas kasar Sin za ta mayar da martani mai karfi don kiyaye 'yanci, da tsaro da ma bunkasuwarta. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China