Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu kula da aikin shawarwari tsakanin Sin da Amurka sun yi musayar ra'ayi
2019-10-26 17:03:10        cri
Manyan jami'ai masu kula da aikin shawarwari kan batun tattalin arziki da ciniki tsakanin kasashen Sin da Amurka, wato mataimakin firaministan kasar Sin mista Liu He, da wakilin kasar Amurka mai kula da harkar cinikayya, Robert Lighthizer, gami da ministan kudin kasar Amurka, Steven Mnuchin, sun yi musayar ra'ayi ta wayar tarho a jiya Jumma'a, inda bangarorin 2 suka yarda da kokarin kawar da damuwar junansu, tare da tabbatar da kammala tattaunawa game da wasu bayanan yarjejeniyar da kasashen 2 za su kulla a karshe, da zummar daidaita takaddamarsu a fannin ciniki. Ban da haka, a wajen tattaunawarsu, jami'an sun cimma ra'ayi daya kan yadda kasar Amurka za ta shigo da nama daga kasar Sin, da daidiata tsarukansu na sa ido kan aikin sarrafa abinci masu alaka da kifi, da yadda kasar Sin za ta soke matakin da ta sanya na hana shigo da naman kaza daga kasar Amurka, da kuma fara amfani da wani tsari na gabatar da bayanai game da ingancin nama, da dai makamantansu. An tabbatar da cewa, wadannan jami'an za su sake yin magana da juna a kwanakin nan. Kafin haka kuma, kananan jami'an dake cikin tawagogin kasashen 2 za su ci gaba da aikin shawarwari. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China