![]() |
|
2019-05-07 06:51:24 cri |
Daraktan UNICEF a kasar mai barin gado, Maniza Zaman ce ta bayyana haka a jiya, lokacin da take ganawa da shugaban Zanzibar, Ali Mohamed Shein.
Maniza Zaman ta yabawa shugaban kasar da gwamnatinsa bisa kokarin da suka yi na takaita cin zarafin mata da take hakkokin yara da kuma yaki da cututtuka irinsu Malaria da kwalara.
Ta kara da cewa, asusun UNICEF zai ci gaba da aiwatar da shirye-shiryensa a Zanzibar, ciki har da tallafawa yara ta fuskar tattalin arziki da sauransu.
A nasa jawabin, Shugaban Zanzibar, ya ce UNICEF na da babban tarihi da Zanzibar a bangaren batutuwan da suka shafi ci gaba, kamar raya bangarorin ilimi da kiwon lafiya, musammam ga mata da yara.
Ya ce Zanzibar za ta ci gaba da aiki da hukumomi daban daban na MDD, ciki har da UNICEF, domin tabbatar da kiyaye hakkokin yara. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China