Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci kasashe da cibiyoyin Afrika su gina tsarin tattalin arziki da zai jure sauyin yanayi
2019-08-27 10:30:08        cri
An bukaci kasashen Afrika da cibiyoyin Afrika da su kara kwazo wajen kafa wani tsarin tattalin arziki a fadin nahiyar wanda zai iya jurewa matsalolin sauyin yanayi.

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ce ta yi kiran a jiya Litinin, a yayin da nahiyar Afrikan ke shirin gudanar da babban taro game da batun sauyin yanayi a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, a cikin wannan mako, wanda aka shirya karkashin hadin gwiwar hukumar AU, da hukumar raya tattalin arzikin Afrika ta MDD (ECA), da bankin raya ci gaban Afrika (AfDB), da hukumar kula da sauyin yanayi ta Afrika.

Babban taron game da sauyin yanayi da ci gaban Afrika (CCDA), wanda za'a gudanar a helkwatar AU dake Addis Ababa daga ranar 28 zuwa 30 ga watan Ogusta, taro ne na musamman game da shirye-shiryen irin gudunmawar da kasashen Afrika za su bayar a taron kolin sauyin yanayi na kasa da kasa, wanda babban sakataren MDD zai jagoranta a ranar 23 ga watan Satumba, AU ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar.

Taron shiyyar na kwanaki uku na wannan karon, mai taken "Daukar matakan jure matsalolin sauyin yanayi ga tattalin arzikin Afrika, rawar da za mu iya takawa don cimma nasara." (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China