Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta damu matuka game da karuwar cin zarafin lalata a yankunan da ake rikici a Afirka
2019-08-02 10:05:40        cri
Kungiyar tarayyar Afirka (AU), ta bayyana matukar damuwa game da karuwar rahotannin cin zarafin lalata a lokutan tashe-tashen hankula a sassan nahiyar Afirka.

Kungiyar mai mambobin kasashe 55, ta bayyana damuwa kan wannan matsala ce, biyo bayan ganawar baya-bayan da hukumar zaman lafiya da tsaron kungiyar ta yi, mai taken, "Cin zarafin lalata a lokutan tashin hankali a Afirka". Hukumar ta bayyana damuwa matuka kan karuwar wannan matsala, duk da kokarin da kasashe mambobin kungiyar ta AU ke yi na kawo karshen wannan ta'asa

Kungiyar ta bayyana cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Alhamis cewa, galibin wadanda ke aikata wannan danyen aiki a Afirka, ba 'yan kasashen ba ne, don haka, ta ce, yana da muhimmanci daukacin kasashe mambobin kungiyar, su sanya hannu, su kuma fito da wata yarjejeniya, wadda za ta hukunta hukumomin AU da na kasa da kasa dake da nasaba da aikata cin zarafin lalata. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China