Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta bukaci zurfafa hadin gwiwa da bangarorin masu zaman kansu don cimma ajandar nahiyar
2019-08-25 16:29:17        cri
Kungiyar tarayyar Afrika AU, ta jaddada muhimmancin zurfafa hadin gwiwa tsakanin masu tsara manufofi na Afrika da bangarorin masu zaman kansu, da nufin cimma nasarar ajandar raya cigaban nahiyar na shekaru 50, wato nan da shekarar 2063.

Kungiyar ta Afrika mai mambobin kasashe 55, ta yi kira ga masu tsara manufofin cigaba na Afrika da bangarori masu zaman kansu, kana ta bayyana aniyarta na shirya taron dandanlin tattaunawa da bangarorin masu zaman kansu na Afrika a watan Nuwamban wannan shekarar da nufin karfafa hadin gwiwa tsakaninsu domin cimma nasarar ajandar samar da dawwaman cigaban nahiyar nan da shekarar 2063.

Taron na wannan karo na dandalin hadin gwiwar bangarorin masu zaman kansu na Afrika, ana sa ran zai janyo hankalin mahalarta sama da 300 wadanda ke da ruwa da tsaki a bangarori masu zaman kansu da masu zuba jari wadanda zasu zo daga shiyyoyi biyar na nahiyar Afirka da ma kasashen Sin, Turkiyya, Amurka, da sauran shiyyoyi.

Kungiyar ta Afrika, ta shirya taron kolin nahiyar na bangarori masu zaman kansu ne da nufin zakulo irin muhimmiyar rawar da fannonin masu zaman kansu zasu taka wajen kawo sauye sauyen cigaban tattalin arzikin Afrika, da kuma aiwatar da ajandar raya Afrika nan da shekarar 2063, musamman, game da irin gudummawar da zata bayar wajen rage fatara ta hanyar zuba jari da samar da guraben ayyukan dogaro da kai.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China