Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar AU ta yi Allah wadai da harin 'yan ta'adda da ya hallaka sojoji 24 a Burkina Faso
2019-08-23 11:09:05        cri
Shugaban hukumar zartaswar kungiyar AU Moussa Faki Mahamat, ya yi tir da harin ta'addanci da ya auku a wani sansanin sojojin kasar Burkina Faso, wanda ya yi sanadiyyar rasuwar dakarun soji a kalla 24.

Mahamat ya sake jaddada kudurin kungiyar AU, na ci gaba da goyon bayan gwamnati da al'ummar kasar Burkina Faso, a kokarinsu na karewa, da yakar ayyukan ta'addanci, da na masu tsattsauran ra'ayi, da ma tasirin su a daukacin sassan kasar.

Jami'in ya kuma nanata matsayar kungiyar, na adawa da duk wani nau'i na ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, yana bayyana bukatar yin hadin gwiwa tsakanin kasashen dake yankin a fannin inganta tsaro, domin kariya da yakar ayyukan ta'addanci cikin hadin gwiwa.

Daga nan sai ya bayyana kwarin gwiwar sa, game da tasirin hadin gwiwar kasashen yankin Sahel, a fannin yaki da ta'adanci, da kuma shirin da aka amince da shi a Nouakchott, na inganta hadin gwiwar tsaro, domin karfafa musayar bayanan sirri a yankin, duka dai da nufin yakar ayyukan ta'addanci da tsattsauran ra'ayi. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China