2019-08-18 16:17:22 cri |
Majalisar sojojin Sudan (TMC) da gamayyar jam'iyyun adawa na Freedom and Change Alliance a jiya Asabar suka rattaba hannu kan yarjejeniyar siyasa da kundin tsarin mulkin kasar, hakan ne ya tabbatar da fara wa'adin gwamnatin rikon kwaryar kasar ta Sudan.
Mataimakin shugaban majalisar TMC Mohamed Hamdan Daqlu, ya sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin majalisar sojojin, yayin da Ahmed Rabie, jagoran Freedom and Change Alliance, ya sanya hannu a madadin gamayyar 'yan adawar.
Wakilin gamayyar Freedom and Change Alliance Mohamed Naji El Asam, yace sanya hannu kan daftarin yarjejeniyar shine ke tabbatar da shiga zagayen farko na yarjejeniyar kafa gwamnatin rikon kwaryar, wanda kuma muhimmin mataki ne na tabatar da zaman lafiyar kasar.
Yace, adalci da kuma tabbatar da ingantaccen tsarin shari'a suna daga cikin muhimman al'amuran da sabuwar gwamnatin rikon kwaryar za ta mayar da hankali kansu.
Shugaban majalisar TMC Abdel-Fattah Al-Burhan, ya jaddada muhimmancin hadin gwiwar dukkan bangarorin al'umma su yi aiki tare don cimma nasarar kawo ingantaccen sauyi a kasar.
Al-Burhan yace, dakarun sojojin Sudan da sauran jami'an tsaron kasar zasu yi iyakar kokarinsu wajen bada kariya ga juyin juya halin kasar domin tabbatar da ganin an maido da mulki hannun fararen hula a Sudan.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China