Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattaunawa tsakanin TMC da 'yan adawar Sudan ta sake gamuwa da cikas
2019-07-30 10:05:29        cri
Rahotanni daga kasar Sudan na cewa, da alamun tattaunawa tsakanin majalisar sojan kasar ta rikon kwarya da bangaren 'yan adawa ta sake gamuwa da cikas, biyo bayan fadan da ya barke jiya Litinin a El Obeid, babban birnin jihar arewacin Kordofan.

Koda yake bangarorin biyu sun fara tattaunawa jiya da safe a birnin Khartoum, domin nazarin muhimman takardun kundin tsarin mulkin kasar, sai dai babu tabbas kan yiwuwar tattaunawa kai tsaye da aka shirya gudanarwa yau tsakanin sassan biyu.

Jaridar Sudan Tribune da ake wallafawa a kasar ta ruwaito cewa, kawancen 'yan adawa ya aike da tawagarsa zuwa Elbeid, domin ya binciko halin da ake ciki bayan tashin hankalin da ya barke a birnin.

A halin da ake ciki kuma, kawancen 'yan adawar ya aike da wata sanarwa, yana zargin majalisar sojan rikon kwaryar kasar da hannu a tashin hankalin da ya faru a El Obeid, yana mai cewa, sojoji da dakarun kai dauki sun harbi mutane har lahira.

A hannu guda, su ma jam'iyyun siyasa a Sudan, sun yi Allah wadai da abin da suka kira "kisan kiyashin El Obeid", inda suka bukaci dakatar da tattaunawa da majalisar sojan kasar. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China