Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan tawayen SPLM a Sudan sun amince da tsakaita bude wuta na watanni 5 a kudancin Kordofan
2019-08-01 10:46:54        cri
Mayakan kwatar 'yancin Sudan na (SPLM) shiyyar arewaci, tsagin Abdel-Aziz Al-Hilu, ta ayyana tsagaita bude wuta na tsawon watanni 5 a kudancin Kordofan.

Al-Hilu ya bayyana cikin wata sanarwa cewa sun dauki wannan mataki ne a matsayin hanyar tabbatar da zaman lafiya game da batun rikicin Sudan, da kuma bada damar mika mulki ga hannun farar hula lami lafiya, ya ce ya ayyana tsakaita bude wutar a yankunan da ake fama da tashe tashen hankula wadanda ke karkashin ikon mayakan.

Sanarwar ta ce, shirin tsakaita bude wutar zai fara ne daga ranar 1 ga watan Agusta zuwa 31 ga watan Disambar wannan shekarar.

Sanarwar ta bukaci dukkan rassan kungiyar ta SPLM arewaci da su mutunta yarjejeniyar tsakaita bude wutar kuma su guji dukkan wani nau'in ta da hankali. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China