Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalissar sojoji da 'yan adawa a Sudan sun sanya hannu kan yarjejeniyar kundin tsarin mulkin kasa
2019-08-05 10:03:46        cri
Majalissar sojoji dake rikon kwarya a Sudan ko TMC a takaice, da gungun 'yan adawa fararen hula a kasar, sun sanya hannu kan yarjejeniyar kundin tsarin mulkin kasa, matakin da zai bude kafar tsara ayyukan gwamnatin rikon kwaryar kasar.

Mataimakin shugaban majalissar sojoji Mohamed Hamdan Daqlu, da jagora a tafiyar 'yan adawa Ahmed Rabie ne suka gabatar da kudurin hakan.

Daga bangaren masu sanya ido kuwa, jakadan kungiyar hadin kan Afirka ta AU Mohamed Hacen Lebatt, da wakilin kasar Habasha Mahmud Dirir, sun sanya hannu kan yarjejeniyar. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China