Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya za ta sanya hannu kan yarjejeniyar AfCFTA yayin taron AU dake tafe
2019-07-03 19:44:56        cri
Fadar shugaban Najeriya ta tabbatar da aniyar gwamnatin kasar, na rattaba hannu kan yarjajeniyar cinikayya maras shinge ta nahiyar Afirka wadda aka yiwa lakabi da AfCFTA, yayin taron gama gari na kungiyar hadin kan Afirka ta AU, dake tafe a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar.

Wata sanarwar da fadar gwamnatin Najeriyar ta fitar ta shafin twitter a jiya Talata, ta ce Najeriya ta amince ta shiga yarjejeniyar AfCFTA ne, bayan duba na tsanaki, da tattaunawa da masu ruwa da tsaki. Kaza lika tana fatan amfani da damar tuntuba da ake yi, wajen tabbatar da ba a yi amfani da yarjejeniyar don yin fasa kauri, da jibge hajoji da sauran kalubale da ka iya biyo baya ba.

Za dai a gudanar da taron gama gari karo 12 na kungiyar AU game da yarjejeniyar ta AfCFTA ne a ranar Lahadi, kamar dai yadda AU ta sanar ta shafinta na yanar gizo. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China