2019-07-02 10:03:36 cri |
Rahotanni daga Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane 7 ciki har da wata mata mai juna biyu biyo bayan wani aikin ceto na gaggawa da aka gudanar don ceto mutanen da ke cikin wani kwale-kwale da ya kife a yankin ruwan Badore-Ijede dake unguwar Ikorodu a jihar Lagos cibiyar kasuwancin Najeriya.
Sai dai hukumar kula da yankin ruwa ta jihar Lagos, ta bayyana cewa, an yi nasarar ceto mutane uku, baya ga wasu mutane 10 da har yanzu ba a ji duriyarsu ba, tun lokacin da lamarin ya faru a ranar Asabar da dare.
Da yake karin haske kan lamarin, babban manajan hukumar kula da hanyoyin ruwan yankin Oluwadamilola Emmanuel, ya sanar da cewa, jirgin mai daukar mutane 20, ya kife ne a tsakiyar teku, bayan da ya ci karo da igiyoyin ruwa da misalin karfe 11 na daren ranar Asabar.
Emmanuel ya ce, binciken da aka gudanar a wurin da lamarin ya faru, ya tabbatar da cewa, hadarin ya faru ne sakamakon rashin kyan yanayi a bangaren matukin jirgin ruwan da kuma rashin sanya rigunan ceton rai a bangaren fasinjoji.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China