Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane a kalla 35 ne suka mutu sanadiyar fashewar tankar dakon mai a Najeriya
2019-07-03 09:56:49        cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, a kalla mutane 35 ne suka mutu kana wasu 101 kuma suka samu raunukan kuna daban-daban, lokacin da wata tankar dakon mai ta yi bindiga ranar Talata a kauyen Ahumbe na jihar Benue dake yankin kudancin kasar.

Da yake karin haske kan lamarin, kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa reshen jihar, Aliyu Baba, ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne lokacin da motar ta kife bayan da ta yi hadari, ta kuma kama da wuta yayin da gomman mutane ke kokarin kwasar man dake malala daga motar.

Baba ya kuma shaidawa manema labarai a Makurdi, fadar mulkin jihar cewa, motar dakon man ta kauce hanya ne lokacin da direban motar ke kokarin kaucewa wani rami a hanyar. Nan take sai motar ta kwace ta kuma kife. An shafe kusan mintuna 45 ana kwasar man dake malala daga motar, har zuwa lokacin da wata motar bas kirar Toyota ta ci karo da motar dakon man, lamarin da ya haddasa fashewa ta farko, inda wuta ta kama ta kuma kashe mutane 14 dake cikin motar bas din nan take, da ma wasu mutane dake kokarin kwasar man.

Fashewa ta biyu kuma wadda ta jikkata mutane da dama, ta faru ne lokacin da wadanda suka je kallon hadarin da ya faru, da masu motoci da kauyawan dake yankin suka taru a wajen da lamarin ya faru ko dai su kashe kwarkwatan ido ko kuma su taimaka a ayyukan ceto. A wata sanarwa da ya fitar, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwa da hasarar rayuwan da a cewarsa za a iya magance ta.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China