Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CBN Zai Rage Yawan kudin Da SuKe kewayawa A Hannun Jama'a
2019-07-01 11:05:30        cri
Bisa labarin da muka samu daga shafin Intanet na jaridar Leadership, babban bankin Nijeriya CBN ya sanar da cewa, zai rage yawan kudaden da suke kewayawa a cikin kasar.

Shugaban reshen babban bankin na CBN na jihar Cross Ribers, Chuks Okafor ne ya sanar da hakan a wani taron bita na kwana biyu da bankin na CBN ya shirya domin inganta hada-hadar kudade da tattalin arzikin kasar.

A cewar Babban Bankin na Nijeriya, ya kudiri aniyyar daukar wannan matakin ne don ya inganta amfani da hanyoyin hada-hadar kudi na zamani.

Babban bankin na CBN ya kuma ce ya fara shirin samarwa manoma da kananan 'yan kasuwa bashi, baya ga wasu shirye-shieyen samarwa 'yan kasuwa kudaden da za su bunkasa kasuwancinsu.

Ya kuma ce ya fara aikin janye tsoffin kudade da ake amfani da su, kana za a hukunta duk wanda aka samu yana lalata takardun kudin kasar, kana bankin yana gab da rage adadin takardun kudaden naira da ke kewayawa a kasar don inganta cinikayya na zamani.

Jami'in ya bukaci 'yan kasuwa da manoma da sauran daukacin jama'a, da su bullo da hanyoyin kasuwanci da za su ci gajiyar shirin tallafi na bankin.

Okafor ya kuma bayyana cewa CBN bai ji dadin yadda wasu 'yan Nijeriya ke cin wulakanta takardar kudin kasar wato naira ba, don haka ya yi kira ga 'yan kasar da su rinka daraja takardar naira.

Shugaban ya kara da cewa CBN ya fara aiki domin kawar da tsoffin takardun naira da ke hannun al'ummar kasar.

A karshe ya shawarci 'yan Nijeriya su rinka sanar da CBN a duk lokacin da suka samu matsala da ma'aikatan bankunansu, domin a warware ta yadda ya kamata.(Leadership Hausa)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China