Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da kashe mayakan Boko Haram da lalata tungarsu a dajin Sambisa
2019-06-18 09:48:59        cri
Rundunar sojin saman Nijeriya ta bayyana a jiya cewa, an kashe wani adadi na mayakan BH, biyo bayan wani matakin soji da aka dauka, wanda ke da nufin lalata tungar kungiyar a yankin arewa maso gabashin kasar.

Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar Ibikunle Daramola, ya ce an kaddamar da aikin na ranar Lahadi ne, bayan rahotannin sirri da na sa ido da bayyanan da aka tattara, sun nuna cewa akwai mayakan BH masu yawa a sabon sansaninsu dake cikin dajin na jihar Borno, dake arewacin kasar.

Dajin Sambisa shi ne sansanin horo mafi girma na kungiyar BH a kasar.

A cewar kakakin rundunar, rundunar ta sojin sama, dake aiki cikin hadin gwiwa da dakarun kasa, za su ci gaba da kokarin karya lagon 'yan ta'addan baki daya a arewacin kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China