2019-06-19 20:15:48 cri |
Da yake karin haske game da harin, dan majalissar dokokin jihar Timothy Datong, ya ce yayin harin na yammacin ranar Litinin, 'yan bindigar sun kone a kalla gidajen kwana 54, kana sun lalata gonaki da dama, lamarin da ya tilasawa mazauna kauyen barin muhallansu.
Mr. Datong ya ce yanayin tsaro a jihar musamman a wannan lokaci na zama mai matukar ban tsoro.
Kawo yanzu dai rundunar 'yan sandan jihar ta ce ba bu cikakken bayani, game ko su waye suka kaddamar da harin, da ma dalilin aukuwar sa. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China