Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Najeriya ya ce ya kadu game da kisan wasu 'yan kasar su 25 a kauyukan jihar Sokoto
2019-06-10 20:28:35        cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kadu ga samun labarin kisan wasu 'yan kasar su 25, mazauna kauyuka uku dake karamar hukumar Rabah ta jihar Sokoto.

Shugaba Buhari wanda ya bayyana hakan a Litinin din nan, ya ce hankalinsa ya yi matukar tashi, da jin cewa wasu 'yan bindiga sun hallaka kauyawa a kalla 25 a jihar ta Sokoto dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.

Harin 'yan bindigar ya auku ne da yammacin ranar Asabar, inda mahukunta suka ce an binne gawawwakin mamatan a jiya Lahadi. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China