2019-06-20 19:57:03 cri |
Mr. Gao Feng ya bayyana hakan ne, yayin taron manema labarai na ranar Alhamis din nan. Ya ce shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaran sa na Amurka Donald Trump, sun zanta ta wayar tarho a ranar Talata, inda Shugaba Xi ya amince da bukatar sassan wakilan cinikayyar kasashen biyu, su ci gaba da tattaunawa game da dabarun warware sabani.
Gao ya ce sassan biyu za su bi umarnin shugabannin kasashen su, wajen tsara zantawa yayin taron kungiyar G20 dake tafe a birnin Osakan kasar Japan.
Gao ya kara da cewa, Sin na matukar adawa da bin manufar bin ra'ayin kashin kai, da kakaba haraji, tare da fadada rashin fahimtar juna ta fuskar cinikayya. Ya ce tuni aka karbi sama da rahotanni 1,500, masu kalubalantar karin harajin, tun bayan da ofishin wakilin cinikayya na Amurka ya fara karbar shawarwari a tsawon mako guda daga ranar Litinin, don gane da shirin Shugaba Trump na karawa hajojin Sin da ake shigarwa kasar sa haraji.
Daga nan sai ya bayyana fatan sa, na ganin Amurka ta saurari mabambantan ra'ayoyi daga tsagin masana'antun al'ummar ta, ta kuma gaggauta kauracewa daukar matakai na kuskure, domin kaucewa karin hasara ga sassan kasuwanni, da masu sayayya na kasashen biyu.(Saminu Alhassan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China