Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a iya kawar da sabani tsakanin Sin da Amurka ta fuskar ciniki ta hanyar tattaunawa
2019-06-19 19:58:35        cri

A yau Laraba ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya ce daddale wata yarjejeniya tsakanin kasashen Sin da Amurka domin moriyar juna, zai dace da moriyar dukkanin jama'arsu, kana kasashen duniya suna alla-alla wajen ganin haka. Ya ce sau da dama Sin ta jaddada cewa, za a iya kawar da sabani tsakanin kasashen 2 ta fuskar ciniki da tattalin arziki ta hanyar tattaunawa.

An labarta cewa, jiya Talata Robert Lighthizer, wakilin Amurka kan harkokin ciniki, ya tabo rikicin da ke tsakanin Amurka da Sin ta fuskar tattalin arziki da ciniki, inda ya ce ba zai yiwu a tattauna da kasar Sin ba.

Dangane da kalaman na sa, Lu Kang ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, jiya shugaba Xi Jinping na kasar Sin, da takwaransa Donald Trump na Amurka, sun zanta ta wayar tarho, inda mista Trump ya ce, Amurka na sa muhimmanci kan hada hannu da Sin ta fuskar tattalin arziki da ciniki, ya kuma yi fatan cewa, tawagogin aikin kasashen 2 za su fara tuntubar juna, a kokarin lalubo bakin zaren warware rikicin cikin hanzari. Ya yi imani da cewa, kasashen duniya na fatan Amurka da Sin za su daddale yarjejeniya.

A nasa bangaren, mista Xi ya yarda da ci gaba da tuntubar juna tsakanin tawagogin aikin kasashen 2. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China