Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dole ne Sin da Amurka su kyautata tunani kan dangantaka tsakaninsu
2019-06-19 11:11:38        cri

Jakadan kasar Sin dake Amurka Cui Tiankai ya bayyana a jiya Talata a Washington cewa, dole ne Sin da Amurka su kyautata tunaninsu yadda ya kamata kan dangantakar dake tsakaninsu, da tsai da tsarin raya huldarsu mai amfani, saboda ita hanya daya tilo da za a iya kare muradun jama'ar kasashen biyu, har ma moriyar daukacin jama'ar duniya gaba daya.

Cui Tiankai ya furta haka ne a gun bikin tunawa da cika shekaru 40 da kafa dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu da Sinawa da'yan kasar Sin dake Amurka suka gudana a Capitol Hill a wannan rana.

Game da yadda za a bunkasa dangantakar kasashen biyu, Mista Cui ya gabatar da shawararsa guda hudu, wato kara fahimtar juna da kaucewar kuskure, gami da mutunta juna da daidaita bambancin ra'ayi, da kuma zabi hanya da ta dace da kara hadin kai, har ma da aza tubali mai inganci da biyan bukatun jama'a.

Ban da wannan kuma, a cewarsa, Amurka da Sin na da moriyar bai daya a maimakon bambancin ra'ayi, akwai yiwuwar hadin kai a maimakon takaddama a tsakaninsu, hadin kansu hanya daya tilo da za su bi kuma ya dace da muradun kasashen duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China