Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guraben ayyukan dogaro da kai a kasar Sin ya zarta kashi 90 bisa 100
2019-06-21 11:19:07        cri

Rahoton shekara da sashen ilmin koyar da sana'o'in dogaro da kai na kasar Sin ya fitar a jiya Alhamis ya nuna cewa, guraben ayyukan da aka samar na sana'o'in dogaro da kai ga wadanda suka kammala karatu a kwalejojin horas da sana'o'i a kasar Sin ya kai kashi 92% a shekarar 2018.

Rahoton, wanda kwalejin ilmin kimiyya ta Shanghai da kamfanin nazarin bincike na MyCOS suka fitar, ya gano cewa, albashin da ake biyan wadanda suka kammala karatun su a kwalejojin sana'o'in dogaro da kai ya karu da kashi 76.2% a cikin shekaru uku bayan kammala karatunsu.

Kashi 60% na wadanda suka kammala karatun sana'o'in dogaro da kai suna aiki ne a matakan farko kamar ayyuka a kanana da matsakaitan kamfanoni, in ji rahoton, ya kara da cewa, kashi daya bisa hudu daga cikinsu suna samun aikin ne a shiyyar yammaci da arewa maso gabashin kasar Sin.

Rahoton ya bayyana cewa, kashi 65% na kwalejojin horas da ilmin sana'o'in dogaro da kai an kafa su ne da nufin bunkasa yankunan karkara da kuma kawar da fatara.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China