Jami'ar Tsinghua da jami'ar Peking sun kara samun matsayinsu a jerin sunayen jami'o'in mafiya kyau a duniya
Kungiyar kula da bada ilmi ta duniya wato QS ta gabatar da jerin sunayen jami'o'in mafiya kyau a duniya a birnin London dake kasar Birtaniya, inda aka bayyana cewa, jami'o'i mafiya kyau 1000 a duniya sun fito daga kasashe da yankuna 82 na duniya. Jami'ar Tsinghua ta kasar Sin ta daga karfinta inda ta zama matsayi na 16 a duniya, kana jami'ar Peking ta kasar Sin ta daga daga matsayi na 30 zuwa na 22. Don haka, jami'o'in biyu na kasar Sin sun zama matsayi mafi gaba a tarihi. Jami'o'in kasar Sin 65 suna cikin jerin sunayen a wannan karo, a cikinsu guda 42 sun zo daga babban yankin kasar Sin, guda 16 daga yankin Taiwan, kuma guda 7 daga yankin Hongkong.
Shugabar sashen Sin na kungiyar QS Doctor Zhang Yan ta yi nuni da cewa, Sin ta kara dora muhimmanci da zuba jari ga nazarin kimiyya da fasaha a duniya, hakan ya inganta karfin fasahohin ilminta sosai, gibin dake tsakaninta da kasar Amurka da Birtaniya a wannan fanni yana raguwa sannu a hankali.
Doctor Zhang ta kara da cewa, Sin tana kokarin raya kasa ta hanyar bada ilmi, tare da hada bada ilmi da yin nazarin kimiyya da fasaha tare. (Zainab)