Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ra'ayin Bankin Duniya game da shawarar "ziri daya da hanya daya" ya yi daidai da na kasar Sin
2019-06-19 20:10:18        cri

Kwanan baya, bankin Duniya ya kaddamar da rahoto mai taken "zarafi da barazana, wadanda shawarar 'ziri daya da hanya daya' ta kawo".

Dangane da rahoton, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana yau Laraba a nan Beijing cewa, bankin Duniya ya bayyana ra'ayinsa cikin rahotonsa, kan sakamakon da aka samu cikin shekaru 6, tun bayan da kasar Sin ta fara raya shawarar "ziri daya da hanya daya", inda kuma ya ba da shawara kan yadda za a tinkari barazanar dake tattare da hakan.

Lu Kang ya ce, hukumomin Sin masu ruwa da tsaki za su yi nazari kan rahoton yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China